Obama ya ce takaicin jamaa ne ya hana jam'iyyarsa samun nasara

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama ya ce shan kayen da jam'iyyar Democrat ta yi a zaben majalisun dokoki na nuni ga irin rashin jin dadin jama'a game da tafiyar haiwainiyar da ake samu wajen farfadowar tattalin arzikin kasar.

Ya ce a matsayinsa na shugaban kasa, ya dauki alhakin matsalar da ake samu wajen kasa samar da ayyukan yi cikin hanzari.

Tuni dai 'yan jam'iyyar Republican suka fara mayar da martani kan matakan da za su dauka bayan nasarar da suka samu ta kama kujeru mafiya rinjaye a majalisar wakilan kasar, ciki kuwa har da soke shirin lafiya na shugaba Obama.