Kotu a Faransa tace a mika dan tawayen Rwanda ga Kotun Laifuka ta Duniya

Alkalan Faransa
Image caption Alkalan Faransa

Wata kotun daukaka kara a Paris ta amince da a mika wani shugaban 'yan tawayen kasar Rwanda ga kotun hukunta manyan laifuka dake Hague.

Ana tuhumar Callixte Mbru-shimana, wanda aka kama a Faransa watan da ya gabata, da aikata laifuka goma shadaya da suka shafi laifukan yaki a jamhuriyar Demokradiyyar Congo bara:

Wakilin BBC yace: Za'a kalli shawarar mikashi ga kotun laifuka din a matsayin wani kyakykyawan mataki daga wadanda sukai ammanar cewa rashin bayyana gaskiya ya taimaka wajen rura wutar yakin gabashin Congo.