Attahiru Bafarawa ya koma jam'iyyar ACN

Alamar jam'iyyar ACN
Image caption Alamar jam'iyyar ACN

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma jigo a jam'iyyar DPP ya yanki katin shiga jam'iyyar ACN a mazabarsa ta Bafarawa dake jihar Sakkwato.

Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce ya yanke wannan hukunci ne domin mutunta yarjejeniyar da yace an cimma a baya da wasu 'yan siyasa na shiga wannan jam'iyya ta ACN.

Sai dai kuma shigar tasa jam'iyyar ACN ta bar baya da kura domin wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar sun ce suna nan Daram a cikin jam'iyyar DPP.

Shi dai Alhaji Attahiru Bafarawa, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2007, karkashin inuwar jam'iyyar DPP, yana fatan sabuwar jam'iyyar tasa ta ACN ta tsayar da shi takara a zaben shugaban kasa na shekara ta 2011.