Ana daukar matakan kariya kan jiragen Airbus

Jirgin Qantas samfurin A380-800
Image caption Jirgin kamfanin Qantas samfurin A380

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Singapore, ya ce yana jinkirta tashin baki dayan jiragen sa samfurin Airbus, domin daukar matakan kariya.

Hakan dai ya zo ne bayan da daya daga cikin jiragen, mallakar kamfanin Qantas na Australia, ya yi saukar gaggawa a kasar ta Singapore.

Singapore Airlines ya ce yana daukar matakan ne bayan da kamfanin na Airbus da kuma masu samar da injinan jirgin Rolls Royce, suka shawarce shi da yayi hakan. Jirgin Qantas - dauke da kimanin fasinja dari hudu da hamsin, ya yi saukar gaggawa a filin saukar jiragen sama na Singapore.

Jirgin wanda ke dauke da fasinjoji kusan dari hudu da sittin, ya taso ne daga Singapore kan hanyarsa ta zuwa Sydney, amma tilas ya juya mitoci shida bayan da ya tashi.

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Australia, Qantas, ya ce babu wanda ya samu rauni a cikin fasinjojin jirgin.