Gwamnoni sun tabbatar da Bukola Saraki

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, Kungiyar Gwamnonin Jihohin kasar ta ce har yanzu Gwamnan Jihar Kwara, Bukola Saraki, shi ne ke shugabancinta, kuma a iya saninta babu wani sabon shugaba da ta zaba.

Bayan wani taro da ta gudanar a daren jiya, Kungiyar ta bayyana cewa ta amince Gwamna Bukola Saraki ya ci gaba da rike shugabancinta har lokacin da za a zabi wani shugaban.

Kungiyar dai ta kafa wani kwamiti a karkshin jagorancin Gwamna Babatunde Fashola na Jihar Legas, wanda ta baiwa makwanni uku don ya duba yadda za a gudanar da zaben sabon shugaban.

Da ya ke zantawa da BBC bayan taron, Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa ya ce gwamnonin sun yiwa juna afuwa dangane da sanarwar da wadansu daga cikinsu suka bayar ta nada Gwamna Gbenga Daniel na jihar Ogun a matsayin shugabansu.

“Ba wanda ya ji dadin wannan abin; su ma dai sun ce a yafi juna...

Ba wani rikici da ya saura a wannan magana; za mu zauna mu tattuna yadda ya kamata a canja shugaba—mun kare wannan maganar”, inji shi.

Shi ma Gwamna Gbenga Daniel ya ce shi fa bai nemi wannan mukami ba.

A makon jiya ne dai wadansu daga cikin gwamnonin suka yi taro, inda suka ce sun zabi Gwamna Daniel a matsayin sabon shugaban Kungiyar, matakin da wadansu gwamnonin suka ce babu hannunsu a ciki.