Babu wanda ya yi nasara a zaben Ivory Coast

Shugaba Gbagbo
Image caption Shugaba Gbagbo na fuskantar babban kalubale

Sakamakon karshe na wucin gadi da aka samu a Ivory Coast ya nuna cewa babu dan takarar da ya samu sama da kashi 50 na zaben da aka yi, don haka sai an je zagaye na biyu.

Shugaba mai ci yanzu Lauren Gbagbo ya samu kashi 38, sannan tsohon Pira minista Alassane Ouatara yazo na biyu da kashi 32 na kuri'un da aka kada.

Tsohon shugaban kasar Henri Konan Bedie shi kuma ya samu kashi 25 na kuri'un da aka kada, amma yace zai kalubalanci sakamakon zaben.

Duk da yake shugaba Gbagbo ne ke kan gaba a zagaye na farko na zabn da aka gudanar, sai dai kuri'un da ya samu sun gaza yadda binciken ra'ayoyin jama'ar kasar ya nuna gabanin gudanar da shi.

Kawancen gamayyar adawa

Yanzu dai zai fuskanci babban kalubale daga gamayyar jam'iyyun adawar kasar, a yayin da a ka zo gudanar da zagaye na biyu na zaben, wanda ake sa ran yi a karshen watan Nuwamba.

Outtara da Bedie, sun kulla kawance a gamayyar jam'iyyun adawa, tare da wasu kananan jam'iyyu,wadanda suka samu kashi 60 na sakamakon a zagayen farko na zaben.

Sai dai babu wani tabbas cewa, Outtara, wanda ya samu kuri'u daga yawanci musulmin da suka fi rinjaye a arewacin kasar, zai samu dukkan kuri'un da aka kadawa Bedie, a gabashin kasar.

Za a ci gaba da samun fadi-tashin siyasa cikin makonnin kalilan masu zuwa, tunda dai shugaba mai ci na neman goyon bayan manya-manyan 'yan adawar kasar.