Abu Hamza ya yi nasara kan gwamnatin Burtaniya

Abu Hamza
Image caption Abu Hamza ya dade yana fuskantar kalubale daga mahukunta

Malamin addinin musuluncin nan na Burtaniya Abu Hamza, ya yi nasara kan karar da ya daukaka bisa matakin gwamnatin Burtaniya na kwace masa takardun zama dan kasa.

Wani kwamitin saurarar karar na musamman daga ofishin kula da shige-da-fice (siac), ya amince dabukatar malamin a wani hukuncin da ya yanke.

Malamin ya bayyana cewa idan har aka kwace masa takardun na Burtaniya, to zai zamo ba shi da kasar da zai zauna, domin tuni kasar Masar - mahaifarsa ta kwace takardunsa na zama dan kasar.

Mai magana da yawun fadar gwamantin Burtaniya ya ce Pira Minista David Cameron, bai ji dadin hukuncin ba, amma yace hakan ba zai hana yunkurin da ake yi na kai malamin Amurka domin ya fuskanci shari'a ba.

Sheikh Hamza, mai shekaru 52, an yanke masa hukuncin shekaru 7 a shekara ta 2006, kan laifin rura wutar tashin hankali da nuna banbancin launi.