An gano rumbun makamai a Jos

'Yansandan Najeriya
Image caption 'Yansandan Najeriya a bakin aikin

A Najeriya, rundunar 'yansandan Jihar Filato ta ce ta gano wani rumbun makamai a Kuru, kusa da Jos, babban birnin Jihar.

Rundunar 'yansandan ta ce ta gano rumbun makaman ne sakamakon wadansu bayanan sirri da hukumomin tsaro suka yi aiki da su kuma tana ci gaba da bincike a kan al’amarin.

Kwamishinan 'yansandan Jihar, Ikechukwu Aduba, wanda ya ce al’amarin abin tsoro ne, ya shaidawa BBC cewa rundunar ta kama mutane hudu masu aiki a rumbun makaman, ko da ya ke madugun su ya ranta a na kare.

“Wannan abu ne mai muni sosai; [an samu] albarusai da zungurun makamai—wannan shi ya sa muka damu—ban san abin da suke so su mayar da Jihar Filato ba”, inji Mista Aduba.

Jihar Filato dai ta yi fama da tashe-tashen hankula na kabilanci da na addini a 'yan shekarun nan inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu.