An kasa gano yarinyar da aka sace a Bauchi

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, rahotanni daga Jihar Bauchi na cewa har yanzu ba a gano wata yarinya da wasu 'yan bindiga suka sace a raanr Alhamis din da ta gabata ba.

An dai sace yarinyar ne yayin da ake tukasu tare da wasu 'yan uwanta su biyu zuwa makaranta da safiyar ranar ta Alhamis.

Sai dai rundunar 'yan sandan Jihar ta Bauchi ta ce, ta tsaurara bincike domin gano inda yarinyar take, da kuma wadanda suka sace ta.

Satar mutane domin neman kudin fansa na dada yawaita a sassa daban -daban a Najeriya.