A Nijar jamiyyar PNDS Tarayya ta tsayar da dan takara

Image caption Masu Zabe a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, jam'iyar PNDS Tarayya ta gudanar da wani babban taro domin tsayar da dan takarar ta a zaben shugabancin kasar da za'a yi nan gaba.

Bayanai daga zauren taron sun bayyana cewa Alhaji Mahamadou Issoufou, wato shugaban Jam'iyar ne aka kaddamar a matsayin dan takara.

Kuma rahotannin na bayyana cewa shi kadai ne, a cikin jigogin jam'iyar ta PNDS Tarayya ya tsaya a matsayin dan takara a zaben shugabancin kasar da ke nan tafe.

A watan Janairun shekarar 2011 ne dai hukumomin Mulkin Sojin kasar su ka ce za'a gudanar da zabe, sannan kuma a rantsar da sabon zababben Shugaban Kasar ranar shida ga watan Afrilu.