An karawa masu sayen NITEL lokaci

Mataimakin Shugaban Najeriya, Namadi Sambo
Image caption Mataimakin Shugaban Najeriya, kuma shugaban majalisar sayar da kamfanonin gwamnati, Namadi Sambo

Hukumomin Najeriya sun baiwa gamayyar wasu kamfanoni da suka sayi kamfanin wayar tarho na kasar, wato NITEL, karin wa'adin wata guda don biyan kudin kafin alkalami na dala miliyan dari bakwai da hamsin domin sayen kamfanin sadarwar.

Hakan dai ya biyo bayan karewar wa'adin da hukumomin suka debawa kamfanonin domin biyan kudin ne amma hakan bai samu ba.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin hukumar da ke kula da sayar da kamfanoni mallakar gwamnatin kasar ta bayyana cewa an kara wa’adin ne bayan nazari da hukumomin kasar suka yi a kan wata wasika da suka samu daga gamayyar kamfanonin.

A cikin wasikar, kamfanoni sun nuna cewa tsauraran dokokin jigilar kudade masu yawa ne suka yi musu dabaibayi wajen biyan kudin a cikin lokacin da aka deba musu.

Rahotanni sun ambato shugabar hukumar, Bolanle Onagoruwa, tana cewa mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo, wanda kuma shi ne shugaban majalisar kula da sayar da kamfanonin gwamnati, ya amince a baiwa gamayyar kamfanonin kwanaki ashirin don su biya kudaden.

Wannan dai shi ne cikas na baya-bayan nan a kokarin sayar da kamfanin na NITEL da hukumomin Najeriya ke yi.

Gamayyar dai, wadda ta kunshi kamfanonin Unicom daga China, da Minerva na Dubai da kuma wani kamfanin Najeriya, ta sayi kamfanin na NITEL a kan kudi dala biliyan biyu da rabi, wanda shi ne tayi mafi tsoka da aka taba yiwa kamfanin tun lokacin da aka fara yunkurin sayar da shi.

Sai dai wasu masana harkar tattalin arziki sun bayyana kokwantonsu dangane da yiwuwar fadawar cinikin a kan wannan farashi wanda suke ganin ya yi yawa matuka.