An gudanar da zabe a kasar Burma

zaben kasar Burma
Image caption masu zabe a Burma

Alummar kasar Burma sun gudanar da babban zaben kasar a karon farko cikin shekaru 20 da suka gabata.

Yan takara masu zaman kansu sun fuskanci matsaloli wurin yin rajista da yakin neman zabe.

An zargi sojojin kasar da yin amfani da wasu jamiyyun siyasa wurin ci gaba da rike madafun iko.

Duk da wannan zargi, masu sharhi kan alamuran yau da kullum sun bayyana cewa, akwai yiwuwar samun nasarar yin zaben.