Wasu tsaffin yan tawayen Niger sun shiga siyasa

Wasu yan tawayen Niger sun shiga siyasa
Image caption Wasu yan tawayen Niger sun shiga siyasa

A jamhuriyar Niger wasu tsoffin yan tawayen Abzinawa a kasar dake yankin AGADEZ a arewacin kasar sun rungumi harkokin siyasa.

Malam Rhissa Feltou, wani kakakin tsohuwar gammayyar yan tawayen kungiyoyin MNJ, da FPN da FFR a kasar Faransa, ya koma Niger watanni kalilan bayan soma tattaunawa da tsohuwar gwamnatin kasar.

Kasar ta Niger dai na shirye-shiryen zabuka da suka hada da zaben yan majalisar dokoki, da zaben shugaban kasa a watan Janairu mai zuwa.

Malam Rhissa Fetou ya bayyana anniyarsa ta sauyawa daga matsayin tsohon dan tawaye, zuwa dan siyasa da zummar taimakawa ga warware rikice-rikice ta hanyar lumana.