Korafi game da shirin zaben Nigeria na karuwa

zaben nigeria
Image caption korafi game da shirin zaben 2011

A Nigeria, yan adawa a kasar na bayyana shakkunsu game da shirye shiryen zaben kasar a shekarar ta 2011.

Yan adawar na ganin har yanzu akwai shirye-shiryenda ya kamata a ce an kammalla in dai ana son ingantaccen zabe, amma kuma har yanzu ba a kammalla su ba.

A yayinda ake ci gaba da gudanar da zabuka a kasashe daban-daban a Afrika da ma kasashen duniya, yan kasar da dama na hankoron ganin cewa Nigeria ta shiga sahun kasashenda aka gudanar da ingantaccen zabe a wannan karo.

Kodayake a ko da yaushe hukumomin kasar na tabbatar da cewa, zabe a shekarar 2011 zai kasance mai inganci, amma mutane kamar Abdulkadir Balarabe Musa na ganin cewa har yanzu ba a yi wasu tanade tanaden tabbatar da hakar ba.