An yi Allah wadai da zaben kasar Burma

Masu zabe a Burma
Image caption Babbar Jam'iyyar adawa ta kauracewa zaben

Kasashen Yammacin duniya sun yi watsi da zaben kasar Burma, wanda shi ne karo na farko da aka gudanar a kasar cikin shekaru ashirin.

Shugaba Obama na Amurka ya bayyana zaben da cewa "babu adalici a cikinsa, kuma bai cimma ka'idojin kasashen duniya ba". Suma kasashen Tarayyar Tuari sun soki zaben.

Sakamakon farko na zaben, ya nuna cewa 'yan takarar jam'iyar da gwamnatin mulkin sojin kasar ke goyon baya ne ke kan gaba.

Sai dai zaben ya ci karo da 'yan matsaloli ga 'yan jam'iyun adawa, inda kuma a ka samu rahotannin karancin mutanen da suka fito don kada kuri'un su.

Babbar jam'iyar fafutikar tabbatar da dimokaradiya ta NLD, wacce Aung San Suu Kyi, ke jagoranta ta kauracewa zaben.

Jared Genser na daya daga cikin lauyoyin da ke kare Auun Suu Kyi, ya kuma shaida wa BBC cewa har yanzu ana kallonta a matsayin wata barazana ga sojojin kasar.

Ya ce:''Tana da matukar farin jini. Ita da magoya bayanta sun lashe fiye da kashi tamanin na kujerun majalisun dokokin kasar da aka gudanar a shekarar dubu da dari tara da casa'in.