CBN ya dakatar da wasu kamfanonin canji

Kudaden Najeriya
Image caption An dade ana sukar yadda ake hada-hadar Kudade a Najeriya

Babban bankin Najeriya CBN, ya bayar da sanarwar janye lasisin manyan kamfanonin canjin kudi wato Bureau de Change da ke da daraja ta daya.

Babban bankin ya ce daukar matakin ya biyo bayan koken da a ke yi na yawaitar fatauci da kudaden kasashen waje da masu canjin ke yi.

Kamfanoni hamsin ne wannan haramci ya shafa, kuma janye lasisin zai fara aiki ne daga ranar Litinin.

Sai dai babban bankin ya ce kasuwannin na iya neman lasisi a karkashin daraja ta biyu, wato ajin da karfin jarinsa bai kai dala miliyan daya ba.