Takaddama a kan cinikin koko a Ghana

Parfesa John Atta-Mills, Shugaban Ghana
Image caption Parfesa John Atta-Mills, Shugaban Ghana

A Ghana wata takaddama ta kaure tsakanin gwamnati da bangaren 'yan adawa, a kan batun cinikin koko.

Takaddamar dai ta samo asali ne bayan da kampanin safarar koko na kasar, watau Ghana Cocoa Board, ya dage haramcin da yayi wa wani kampanin Birtaniya, Amarjaro Holdings, na sayen koko a cikin kasar ta Ghana.

A cikin watan Afrilun da ya wuce ne Ghana Cocoa Board ya aza hanin a kan kampanin na Amarjaro tare da wasu kampanonin guda biyu, bayan da ya zarge su da hannu a harakar fasa-kwabrin kokon zuwa Ivory Coast.

A wata sanarwa da ta fitar, babbar jam'iyyar adawa ta NPP, ta yi kiran da a gudanar da bincike kan lamarin.