An sace ma'aikatan mai 5 a Najeriya

masu fafutuka
Image caption Yankin Niger Delta ya dade yana fuskantar tashin hankali

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani injin hakar mai a yankin Niger Delta, inda suka yi a wan gaba da ma'aikata biyar.

Kamfanin Afren, wanda ke aikin hakar man, ya ce an kuma jikkata ma'aikata biyu a harin. Sai dai ba a bayyana ko 'yan wacce kasa ba ne.

Harin ya zo ne a daidai lokacin da aka aikewa 'yan jarida sakon e-mail ana gargadin kai hari a yankin Niger Delta.

Tashin hankali dai ya yi kasa a yankin mai arzikin mai, tun lokacin da babbar kungiyar masu fafutukar yankin ta amince da shirin afuwa na gwamnatin kasar.

An dauke wadanda suka jikkata

Kamfanin na Afren PLC - wanda ke da hedkwata a London, ya ce 'yan bindiga sun kuma kai hari kan wani jirgin ruwa, sai dai ya ce duka jirgin da kuma injin wadanda ke yankin Okoro da ke gabar ruwan Akwa Ibom, suna hannun sa a yanzu.

Ya kara da cewa an dauke wadanda suka jikkata a jirgi mai saukar ungulu zuwa asibiti.

Kamfanin bai bada wani karin bayani ba, amma ya ce ya dakatar da ayyukan hakar man.

A baya tashe-tashen hankula a yankin Niger Delta sun haifar da koma baya ga adadin man da Najeriya ke hakowa, har sai da gwamnati ta yi tayin afuwa ga dubban masu fafutuka a yankin.

Sai dai an zargi wata kungiyar masu fafutuka da laifin kai harin bom din da ya hallaka mutane da dama a Abuja, a ranar da kasar ke bikin cika shekaru 50 da samun 'yancin kai.