Pakistan ta soki Obama a kan goyon bayan India

Shugaba Obama
Image caption Jawabin nasa zai dadadawa 'yan kasar rai, ganin cewa sun dade suna bukatar wannan kujera

Shugaba Obama ya bayyana goyon bayan India baya a kokarin da take na samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da yaiwa majalisar dokokin kasar ta India a karshen ziyarar kwanaki ukun da ya kai,

Shugaba Obama ya ce, "A shekaru masu zuwa ina sa ran ganin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi wa sauyin ya kasancewa Indiya na cikinsa a matsayin wadda ke da kujerar dindindin."

Sai dai kuma Pakistan ta soki wannan mataki tana mai cewa rawar da makwabciyarta ke takawa a rikicin da ake kan yankin Kashmir goyan bayan ba zai wani tasiri ba. Masu aiko da rahotannin sun ce India za ta yi farin ciki game da samun goyan baya wajen samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro da take ta godon samu.