Bush ya kare matakin mamaye Iraqi

George Bush
Image caption Littafin shugaban Amurka George Bush

Tsohon shugaban kasar Amurka George W. Bush, ya kare matakan da ya dauka na mamaye Iraqi.

Bush ya shaida wa gidan talabijin na NBC cewa, duk da yake ba a gano makaman kare dangi lokacin da Amurka ta mamaye Iraqi, bai yi da-na-sanin daukar matakin ba. Ya yi kokarin kare matakin da ya dauka na azabtar da mutane da ruwa da aka yiwa wasu da ke tsare, inda ya ce daukar matakin ya taimaka wajen tserar da rayukan mutane, da hana aikata ta'addanci.

Ya ce da zai sake zama shuagaban Amurka, to lallai zai kara bayar da umarnin amfani da hanyar don samun bayanai daga firsinoni.

Ya ce duniya ta zauna lafiya tunda yanzu babu Saddam Husaini a doron kasa.