Shugaba Lula na ziyarar ban kwana a Afrika

Shugaba Lula
Image caption Shugaba Lula a ziyarar da ya kai Muzambique

Shugaban Brazil Inacio Lula da Silva na ziyarar kwanaki biyu a kasar Mozambique domin yin ban kwana da nahiyar Afrika wacce ya baiwa mahimmanci a gwamnatinsa.

Ziyarar ta kwanaki biyu, an shirya ta ne domin fito da irin kyawawan manufofin da Brazil ta dade tana kullawa da nahiyar Afrika karkashin jagorancin shugaba Lula.

Sai dai matakin shugabar kasar mai jiran gado Dilma Rousseff na kin biyo shi, ya rage wa ziyarar armashi.

Mista Rousseff, ta ce za ta hadu da shugaban ne a birnin Seoul lokacin taron kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki.

A watan Janairu ne Dilma Rousseff za ta karbi shugabancin kasar, sai dai babu tabbas ko za ta iya ci gaba da martaba nasarorin da Mista Lula ya samar a shekaru 8 tsakanin Brazil na nahiyar Afrika.

Yawaita ziyara

Daga shekarar 2003, shugaba Lula, ya ziyarci kusan rabin kasashen Afrika a lokuta 12 - fiye da baki dayan shugabannin da ya gada.

Adadin ofisoshin jakadancin Brazil a nahiyar ya ninka zuwa 35. Yayinda huldar kasuwanci ta ninka sau biyar zuwa dala biliyan 26 a bara.

Lula ya ce dangantaka tsakanin Brazil - wacce tafi kowacce kasa a wajen Afrika yawan bakar fata a duniya - da kuma nahiyar Afrika ba wai magana ce ta kasuwanci ba kawai.

Shugaba Lula ya sanarar da kafa wani tsarin ilimi na yaki da jahilci wanda ke da nufin samarda digiri ga mutane 620 nan take - da kuma 7,000 a nan gaba.

Sannan ya kaddamar da wani kamfani a Mozambique da zai fara hada magungunan yaki da cutar kanjamau a badi.

Sabuwar dangantaka

Kusan kasashen Afrika 34 ne suka amfana daga ayyuka 250 da Brazil ta ke gudanarwa, a cewar mahukuntan Brazil.

A yanzu Brazil ta zamo daya daga cikin kasashen da suka fi tallafawa matalautan kasashe a Afrika da yankin Caribbean da kuma Timo ta Gabas.

Jakadan Brazil a Mozambique Antonio de Souza e Silva, ya ce rawar da kasar ke takawa a Afrika za ta dore, ganin karfin tattalin arzikinta da kuma matsayin da take da shi a duniya. "Manufar huldar kasashen waje manufa ce ta kasa. Gwamnatoci za su iya kawo wasu 'yan sauye-sauye kadan, amma ainahin manufofin ba za su sauya ba", kamar yadda ya shaida wa BBC.