Kungiyar D8 za ta fuskanci kalubalen sifirin ruwa

A Najeriya an bude wani taron kwararru akan tafiyar da sufurin jiragen ruwa na kasashen kungiyar D8 masu yawan al'ummar musulmi.

Taron dai zai fi maida hankali ne akan yadda za'a shawo kan manyan kalubalen dake kawo cikas ga karfafawa da kuma saukaka hada-hadar kasuwanci ta sufurin ruwa tsakanin kasashen.

Taron zai kuma bada damar musayar dabarun gudanarwa da kuma kulla zumunta ta fuskar sufurin ruwa tsakanin kasashen na kungiyar ta D-8, ganin cewa daya daga cikin kasashen kungiyar, wato INDONESIA ita ce tafi kowacce kasa yawan tashoshin jiragen ruwa a duniya.

Yanzu haka dai Najeriya ce ka jagorantar kungiyar kasashen na D-8, wadanda suke da dimbin yawan jama'a da kuma manyan kalubale na zamantakewa da kuma tattalin arziki.