Dalibai sun yi zanga zangar tada hankali a London

Zanga zangar dalibai a London
Image caption Zanga zangar dalibai a London

Rikici ya barke a lokacin wata zanga zanga da dalibai su ka yi a London, akan karin kudin jami'a a Ingila.

Dubban dalibai da malamai ne suka gudanar da zanga zangar nuna kin amincewarsu da shirin gwamnati na tsuke bakin aljihu, wanda a karkashinsa, zata rage kudaden da take ba jami'o'i.

Za a kuma rubanya kudin da dalibai ke biya har sau uku - wato zuwa sama da dala dubu 14 a shekara.

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun kutsa kai cikin harabar hedkwatar jam'iyyar Conservative mai mulki, inda suka yi taho mu gama da 'yan sanda.

Shugabannin kungiyar daliban sun yi Allah wadai da tashin hankalin da aka samu.