Cameron na son ganin bunkasar siyasa a China

Pira ministan Burtaniya David Cameron
Image caption David Cameron yana gabatar da jawabi ga dalibai

Pira ministan Burtaniya David Cameron ya ce yana maraba da irin ci gaban da kasar China take samu a duniya, sannan yana fatan za a samu budi a harakokin siyasar kasar.

Mista Cameron ya ce Burtaniya tana da bambance-bambance a kan batun hakkin bil'adama da China, amma duk da haka za a iya kulla kawance kan habakar tattalin arziki.

A cewar David Cameron, China babbar kasa ce a duniya ba kawai ta fuksar tattalin arziki ba, har ma ta fuskar siyasa.

Ya kuma jaddada cewa Burtaniya da China na da buri guda wajen bunkasa cinikayya , da kuma aiki tare don kawo daidaito a tattalin arzikin duniya.

'Fatan samun sassauci'

Sai dai a jawabin da ya gabatar ga dalibai a birnin Beijing, Mista Cameron ya kuma ce karfin tattalin arziki da na siyasa na tattare da alhaki, kuma al'ummar Burtaniya sun kasa kunne su ji ya fayyace bambance-bambancen da ke tsakanin kasashen biyu ta fuskar kare hakkin dan Adam.

Ya ce yana fatan sassaucin da aka samu a China ta fuskar tattalin arziki zai kai ga sassauci ta fuksar siyasa nan da wani lokaci.

Mista Cameron ya ce ba wani boye-boye, mun sha bamban a kan wasu batutuwa, musamman ma kare hakkin bil-Adama.

Ba a dai nuna wannan jawabin kai tsaye a China ba, kuma Mista Cameron ya yi taka-tsantsan wajen gabatar da shi.

Ziyarar ta Mista Cameron ta kai ga cimma yarjeniyoyin cinikayya na sama da dala miliyan dubu dari.