Kungiyar kwadagon Najeriya ta janye yajin aiki

Gine-ginen gwamnati babu kowa
Image caption Jama'a sun kauracewa wuraren aiki a Sokoto

Hadaddiyar kungiyar kwadago ta Najeriya ta janye yajin aikin da ta kira domin neman gwamnatin kasar ta kara musu albashi.

A wani taron manema labarai da kungiyar kwadago ta NLC da kuma ta 'yan kasuwa TUC, suka kira a Abuja, sun bayyana cewa yajin aikin zai zo karshe ne daga karfe 12 na dare.

Kungiyoyin kwadagon sun ce, sun samu tabbaci daga gwamnatin Najeriya cewa da zarar an yi taron majalisar kasa, za a mika daftarin doka ga majalisun tarayya domin aiwatar da sauye-sauyen da suke bukata.

Sun kara da cewa sun samu tabbaci daga majalisun kasar cewa za su gaggauta zartar da kudurin dokar.

Zanga-zanga

Tunda farko sai da 'ya'yan kungiyar kwadago da masu fafutukar kare hakkin bil'adama suka gudanar da zanga-zangar goyon baya ga yajin aikin da suka fara a ranar Laraba.

Image caption Tituna sun dade a wasu sassa da dama na kasar

Zanga-zangar wacce aka gudanar a babban birnin kasuwancin kasar na Legas, an shirya ta ne domin tallata bukatun ma'aikatan Najeriya.

Kungiyoyin sun karade hanyoyin jihar Legas inda suke ta shelar 'yan Najeriya su fito dan yaki da manufofin gwamnatin da suka kira marasa alfanu ga talakawa.

Makarantu da bankuna da ofisoshin gwamnati sun kasance a rufe, yayinda a Legas, motocin haya na gwamnati da dama ba su fito aiki ba.

Tattaunawar da aka yi tsakanin shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Jonathan da shugabannin kwadagon a ranar Talata ta tashi baram- baram.

'Yan kungiyar kwadagon na bukatar gwamnatin tarayyar Najeriyar ce ta biya naira dubu goma sha takwas a matsayin albashi mafi karanci ga ma'aikata.