Hukumar SSS ta zargi Henry Okah da kai hari a jahar Delta

Henry Okah
Image caption Henry Okah

A Najeriya, hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, tace tsohon madugun 'yan gwagwarmayar yankin Niger Dela, Henry Okah, shine ke da alhakin kai wasu tagwayen hare hare a watan Maris din da ya gabata, a Warri, a jihar Delta.

Hukumar ta bayyana haka ne a taron manema labaran da ta kira yau a Abuja, inda ta zargi Henry Okah da cewa shi da kansa ya sanya bama baman da suka tashi a motoci biyu.

Henry Okah dai a halin yanzu yana fuskantar shari'a a kasar Afrika ta Kudu, bisa zargin shine ya tsara hare haren da aka kai a Abuja a ranar daya ga watan Oktoban da ya wuce, ranar da Najeriyar ke bikin cika shekaru 50 da samun mulkin kai daga Birtaniya.