Bikin tunawa da ken Saro Wiwa

Ken Saro Wiwa
Image caption A shekarar 1995 ne aka rataye Ken Saro-Wiwa

An gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da aka kashe tsohon mai fafutukar neman 'yancin yankin Naija-Delta, kuma dan fafutukar kare muhalli Ken Saro Wiwa.

Fiye dai da Shekara Ashirin da suka wuce ne, wasu 'yan kabilar Ogoni da ke Jihar Ribas Karkashin Jagorancin Marigayi Ken Saro Wiwa suka fara kokarin ganin sun kwato 'yancin Al├║mmomin su.

Zargin da masu fafutukar da suka yi shi ne na lalata musu muhalli da Ma'aikatun hakar danyen man fetur suke yi, ba tare da an biya su diyya ba.

A shekarar 1995 ne, a lokacin gwamnatin Janar Sani Abacha mai ritaya aka yankewa dan fafutukar hukuncin kisa bayanda aka same shi da laifin kisan kai.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama ciki harda Amnesty International sun yi Allah wadai da kisan nasa.