An yi watsi da karar Aung San Suu Kyi

Aung San Suu Kyi
Image caption Aung San Suu Kyi ta dade tana fafutukar siyasa a Burma

Kotun koli a kasar Burma ta yi watsi da karar da mai fafutukar dimukuradiyya ta kasar Aung San Suu Kyi, ta shigar game da daurin talalar da aka yi mata.

Kotun bata bayar da wani dalili na watsi da wannan daukaka kara ba, kan hukuncin da aka yanke mata wanda ya sa take zaman talalar na tsawon shekaru 15 cikin shekaru 21 da suka gabata.

Hukuncin dai zai kare ne a ranar Asabar mai zuwa.

Lauyan Aung San Suu Kyi ya ce ba za ta amince da duk wani sharadi da zai hana ta shiga harkokin siyasa ba idan an sallameta.

A halin yanzu dai daurin talala na uku da aka yi mata ya kusa zuwa karshe. Tun shekarar 2003 ne dai aka fara kaddamar da daurin talalar a kanta, aka kuma rika kara tsawon lokacin daurin a watan Mayun ko wacce shekara.

Kuma a watan Agustan shekarar 2009 ne kawai aka yanke mata hukunci a kan saba ka'idojin daurin talalar, lokacin da wani ba Amerike, John Yettaw, ya yi linkaya zuwa gidanta ba tare da ta gayyace shi ba.

Wannan hukuncin ne dai lauyoyinta suka yi ta kokarin ganin an yi watsi da shi, amma ba su yi nasara ba.