An amince da sabuwar gwamnati a Iraqi

Gwamnatin Iraqi na ganawa
Image caption Nouri Maliki da Jalal Talibani za su ci gaba da zama Pira minista da shugaban kasa

Manyan jam'iyyu a iraqi sun cimma yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnati, watanni 8 bayan kammala zabe, a cewar mutumin da ke jagorantar taron.

Shugaban yankin Kurdawa Masoud Barzani, ya bayyana yarjejeniyar da cewa "hada kan kasa ce".

Ya ce Nouri Maliki, wanda dan shi'a ne zai ci gaba da kasancewa a matsayin Pira minista, yayinda 'yan bangaren Sunni za su samu mukamin shugaban majalisa.

Sannan shugabansu Iyad Alawi ya jagoranci majalisar tsare-tsaren ci gaban kasa.

"Mun godewa Allah"

Yayinda Kurdawa za su samu mukamin shugaban kasa.

Image caption Shugabannin siyasar Iraqi na tattaunawa

Ana saran majalisar dokokin kasar za ta gana a ranar Alhamis da yamma.

"Mun godewa Allah, a daren jiya mun cimma babbar nasara, kuma nasara ce ga jama'ar Iraqi baki daya,"a cewar Mista Barzani wanda ke magana a wurin taron manema labarai.

Amma wakilin BBC a Iraqi Jim Muir, ya ce babu tabbas ko mista Alawi zai karbi mukamin - ko kuma hukumar za ta iya taka rawa sosai kan irin matakan da gwamnati za ta dauka musamman ta fuskar tsaro.

Sannan yace ana saran gwamantin hadin guiwar za ta rage almubazzaranci da sabawa doka daga kowacce kungiya, Amurka ta bayyana yarjejeniyar da cewa "babban mataki ne na ci gaba".

Akwai isasshen lokaci

Bangaren Mista Allawi za kuma su samu mukamin ministan harkokin waje. Shugabancin kasar ana saran zai zauna a hannun shugaban Kurdawa Jalal Talabani.

Da zarar majalisar ta zauna ana saran za ta fara da zabar shugaba da mataimaki.

Sannan ta zabi shugaban kasa, wanda zai gayyaci zaman majalisar hadin guiwa mafi girma.

Sannan za a bashi wata guda domin kafa cikakkiyar gwamnati.

Sai dai, wannan ba zai dauki lokaci ba ganin cewa an kammala tattaunawa, a cewar weakilin mu.

Minta Maliki ya samu kwarin guiwa ne a watan Okotoba, bayanda malamin shi'ar nan Moqtada Sadr ya ce zai bashi goyon bayan kujeru 40 din da yake da su a majalisar domin ya nemi zagaye na biyu.