Bom ya yi mummunar barna a Pakistan

Harin bom a Pakistan
Image caption Zaman lafiya a buwayi birnin Karachi

Wani bom mai karfin tsiya ya rugurguza wani rukunin ofisoshin ‘yan sanda a wani yanki mai matukar tsaro a garin Karachi da ke kasar Pakistan, inda ‘yan sandan da ke binciken masu kai hare-hare suke.

‘Yan sanda sun bada tabbacin rasuwar akalla mutane goma sanadiyyar harin yayin da wasu mutane arba'in kuma suka jikkata.

Wadanda suka shaida harin sun ce wata mota ce ta yi kokarin rusa katangar rukunin ofisoshin, abinda ya yi sanadiyyar musayar wuta kafin daga ta kai ga tarwatsewa.

Tun daga watan Disamban bara dai daruruwan mutane ne suka rasu sanadiyyar kashe-kashen siyasa da kuma hare-haren yan bindiga a garin na Karachi.