An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2010 - An wallafa a 16:42 GMT

Ra'ayi Riga: Zubar da ciki ta haramtacciyar hanya

mace na jimami

Wata mace na jimamin mutuwar 'yar uwarta ta hanyar zub da ciki

Kwararru sun bayyana cewar kimanin mata dubu sittin da bakwai ne ke mutuwa a kowacce shekara wurin zubar da ciki ta haramtacciyar hanya, kuma yawancinsu daga nahiyar Afrika suke.

Shin yaya girman matsalar take a yankinku?

Kuma ta yaya kuke ganin za a iya shawo kan wannan matsalar?

Kadan kenan daga cikin tambayoyin da za mu yi kokarin amsawa tare da ku a cikin shirin Ra'ayi Riga na wannan makon.

Idan kuna son shiga cikin shirin, sai ku aiko da takaitaccen ra'ayi da kuma lambar ku zuwa adireshinmu na e-mail: wato hausa@bbc.co.uk, ko kuma ta lambar waya 44 77 86 20 20 09, ko kuma ta dandalinmu na musayar ra'ayi da muhawara wato BBC Hausa Facebook, wanda za ku iya samu a shafinmu na intanet, wato bbchausa.com.

Za kuma ku iya bayyana ra'ayinku ta gurbin da ke kasa:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.