An fara taron G20 a Seoul

Shugaba Obama da David Cameron a taron G8
Image caption Shugabannin kasashen 20 sun fara isa birnin Seoul na Koriya ta Kudu

An fara taron kungiyar kasashe mafiya karfin tattalin arziki ta G20, a Seoul babban birnin Koriya ta Kudu, inda ake saran manufofin kudi za su mamaye agendar taron.

Taron wanda ake yi shekara-shekara zai kuma duba irin ci gaban da kasashen suka samu kan alkawuran da suka dauka na karfafa ka'idojin aikin banki da kuma hada-hadar kasuwannin kudade.

Biyo bayan mummnar matsalar tattalin arzikin da duniya ta fuskanta shekaru biyu da suka wuce.

Mahalarta taron da suka hada da shugabannin kasashen 20, dana bankuna da majalisar dinkin duniya da hukumar lamuni ta IMF da bankin duniya, za su maida hankali ne kan ci gaban da aka samu abisa matakan da suka dauka a baya.

Kawar da talauci

Matakan dai sun hada da yadda bankuna za su samu jari mai kwari domin tsayawa da kafafuwansu, ta yadda ba za su dogara da gwamnatoci ba, koda kuwa an shiga matsalar tattalin arziki.

Akwai kuma hukumar da aka dorawa alhakin samarda hanyoyin da za a karfafa hukumomin kudi, wadda za ta gabatar da rahoto da zai maida hankali kan wasu manyan bankuna 30 a duniya, wadanda rushewarsu ka iya hargitsa tattalin arzikin duniya baki daya.

Har ila yau taron na G20 zai duba hanyoyin tallafawa kasashe matalauta domin rage talauci a duniya, kamar yadda sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya yi alkawari.

Yace: "a matsayi na sakataren majalisar dinkin duniya, zan yi iya kokari na domin tabbatar da cewa shugabannin kasashen da suka fi karfin tattalin arziki sun fito da wasu hanyoyi don samar da sa'ida ga mutanen da suka fi talauci a duniya".

Kasar ta Koriya dai na da alaka ta kut da kut da kasashen Afrika irinsu Ghana da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, inda take zuba miliyoyin daloli a harkokin hakar ma'adanai da sufuri ta ruwa.

An kafa kungiyar ta G20 ne a 1999, kuma ta kunshi kasashe 8 da suka fi karfin arzikin masana'antu da kuma kasashe masu tasowa, irin su Brazil da Koriya da India.