Tarihin Dede Ayew

Dede Ayew
Image caption Dede Ayew ya taimakawa Ghana sosai a bana

Andre ‘Dede’ Ayew’ ya yi saurin haskakawa a fagen kwallon kafa, amma duk da haka ya fuskanci kalubale.

Dan wasan mai shekaru 21, ya fito daga gida mai martaba, domin mahaifinsa Abedi Pele ya zamo zakaran kwallon Afrika har sau uku, yayansa Kwame Ayew, ya buga wa Ghana kwallo har ma ya wakilce ta a gasar Olympics ta 1992.

Rawar da ya taka a gasar cin kofin kasashen duniya ta 2010, ta bayyana yadda ya kware a fagen tamola.

Kuma hakan ya biyo bayan rawar da ya taka ne a gasar cin kofin kasashen Afrika da ma gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 20, inda ya jagoranci Ghana suka lashe kofin a karon farko daga nahiyar Afrika.

Shekara guda kafin haka labarin ya sha banban.

Daukar sa da kociyan Ghana na wancan lokacin yayi ta jawo kace-nace a kasar, kuma bayan da ya kasa tabuka komai a gasar cin kofin kasashen Afrika, surutun ya karu.

Amma ya nuna kansa, inda daga aro kungiyar Arles Avignon, yanzu kociya Didier Deschamps ya amince da shi inda yake amfani da shi koda yaushe a kungiyar Marseille.

A kakar bana ya zira kwallaye hudu. Ganin cewa tun yana dan shekaru 21, ya bugawa kasarshi wasanni 29, akwai alamun akwai sauran tafiya a gaba.

Ra'ayin kwararru kan Dede Ayew

Idan har akwai wani dan wasa da ya nuna jajircewa, to ba zai wuce Dede Ayew ba.

Kusan shekaru uku da suka wuce ba a jin duriyarsa lokacin da yake bugawa tawagar Ghana ta ‘yan kasa da shekaru 17.

Da yawa sun zaci yana amfani da sunan gidansu ne wajen samun alfarma domin bugawa Ghana wasa.

Amma daga baya sun fahimci zancen ba haka yake ba.

Shi ya jagoranci tawagar ‘yan kasa da shekaru 20 na Ghana suka lashe gasar cin kofin duniya a 2009.

Kuma nan take sai ya zamo kusa a tawagar Black Stars, inda ya taimkawa kasar ta kai wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika a karon farko cikin shekaru ashirin.

Dan wasan na Marseille mai shekaru 21, ya kara nuna kansa a gasar cin kofin duniya da aka kamala a Afrika ta Kudu, inda sau biyu yana zamowa dan wasan da ya fi taka leda.

Kuma an saka shi a jerin ‘yan wasa matasa da suka fi kowanne taka rawar gani a gasar, inda ya zo na biyu bayan Sami Khedira na Jamus.

Don haka dan wasan yana taka rawar gani – abinda yasa ya cancanta a bashi kyautar zakaran dan kwallon Afrika na BBC a bana.

Za ku iya zaban ne ta hanyar latsa wannan rariyar likau din da ke biye:

http://www.bbc.co.uk/worldservice/africa/2010/11/101111_afoy_2010_vote_page.shtml

Ko kuma ta lambar waya +44 7786200070