Darajar hannayen jari ta daga a Turai

Tutar Tarayyar Turai
Image caption Tarayyar Turai ta dade tana fama da matsalar tattalin arziki

Darajar hannayen jari a nahiyar Turai ta dago kadan, bayan da ta yi mummunar faduwa sanadiyyar fargabar da masu hada-hada ke da ita game da tattalin arzikin wasu kasashe.

Wakilin BBC ya ce tsawon lokaci dai manazarta na hasashen cewa Ireland na cikin halin matsin da zai iya kai ta ga neman tallafi daga gamayyar Turai irin wanda aka yiwa kasar Girka. Sai dai a wani yunkuri na bai wa masu zuba jari kwarin gwiwa, gwamnatocin kasashen Turai biyar sun bada sanarwar cewa a shirye su ke da su ba da duk wani tallafin kudi da ake bukata.

Kasashen nahiyar Turai da dama na fama da gibi a kasasfin kudinsu, abinda yasa su daukar matakan tsuke bakin aljihu.