Hajjin bana: An hana wasu maniyyatan Ghana biza

Taswirar Ghana
Image caption Maniyyatan Ghana sun dade suna fuskantar matsala

Kimanin wasu maniyyatan kasar Ghana 600 ne aka hana bizar zuwa birni mai tsarki inda suke can zube a sansaninsu dake birnin Accra.

Rahotannin dake fitowa daga wajen dai sun ce ofishin jakadancin Saudi Arabia da ke birnin na Accra ya daina bada bizar saboda adadin da aka ware ma mahajjatan Ghana ya cika.

Adadin maniyyatan na Ghana dai ya kai dubu biyu da dari biyar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da maniyyata daga kasar ta Ghana ke fuskantar matsaloli ba.

Ko a bara ma wasu sun koka da rashin samun tafiya kasar ta Saudiyya domin sauke faralli.

A ranar Litinin mai zuwa ne wato 9 ga watan Zulhijja wanda ya zo dai dai da 15 ga watan Nuwamba za'a hau arfa.