Tarihin Asamoah Gyan

Asamoah Gyan
Image caption Asamoah Gyan ya taka rawa sosai a kakar wasanni ta bana

Asamoah Gyan ya taka rawar da ta fi kowacce a rayuwar sa ta kwallo ne, a gasar cin kofin duniya da kuma ta kasashen Afrika.

Ya fara ne da taimakawa Ghana wajen kaiwa wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika inda Masar ta doke su da ci 1-0.

Bayan da ‘yan wasa irinsu Stephen Appiah da Sulley Muntari da John Mensah da Michael Essien suka kasa halartar gasar saboda rauni, tawagar Ghana to dogara ne kan Gyan.

Kuma dan wasan ya nuna kwazo inda ya zira uku daga cikin kwallaye hudun da Ghana ta zira wadanda suka bata damar zuwa wasan karshe a karon farko cikin shekaru 18.

Gyan ya ci gaba da haskakawa inda ya zira kwallaye ukun da suka taimakawa Ghana ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin duniya.

Kuma ya zamo dan Afrika na biyu da ya zira kwallaye a gasar cin kofin duniya, baya ga dan Kamaru Roger Milla.

Sai dai rawar da yake takawa bata tsaya a Ghana ba kawai.

Ya zira kwallaye 13 a kungiyarsa ta Rennes da ke Faransa.

Kuma hakan ne yasa kungiyar Sunderland ta Ingila ta saye shi da kudade masu yawa, kuma ba tare da bata lokaci ba ya fara nuna kansa a wasan da suka buga da Wigan.

Sai dai fannaretin da ya baras a wasansu da Uruguay ya hana Ghana zamowa kasar Afrika ta farko da ta kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya.

Duk da cewa ana yi masa kallon bai shahara sosai ba, hukumar FIFA ta sanya shi a jerin ‘yan wasa 23 da za a zabi zakaran dan kwallon duniya daga cikinsu.

Ra'ayin kwararru - da Ibrahim Sannie

Ta hanyar la’akari da rawar da ya taka a kasarsa da kuma kungiyarsa a shekara ta 2010, ina ganin babu wanda ya fi cancanta ya samu kyautar zakaran dan kwallon Afrika na BBC a bana kamar Asamoah Gyan.

Duk da cewa wasu za su iya fifita ‘yan wasa irinsu Didier Drogba na Chelsea da Samuel Eto’o na Inter Milan saboda girman kungiyoyin da suke taka leda.

Amma idan aka lura sosai za a ga cewa kokarinsu ya fi karkata ga kungiyoyinsu.

Yayinda Gyan ya fita zakka inda ya zamo dan wasa daya tilo da ya kai Ghana wasan karshe a gasar cin kofin kasashen Afrika.

Dan wasan, mai shekaru 25, ya nuna kwazo inda ya zira uku daga cikin kwallaye hudun da Ghana ta zira wadanda suka bata damar zuwa wasan karshe a karon farko cikin shekaru 18.

Gyan ya ci gaba da haskakawa inda ya zira kwallaye ukun da suka taimakawa Ghana ta kai wasan dab da na kusa da karshe a gasar cin kofin duniya. Yayinda wadanda ake ganin suna da ‘yan wasa sosai suka kasa kaiwa ko’ina.

Ya zira kwallaye 13 a kungiyarsa ta Rennes da ke Faransa-abinda yasa ya zamo na biyar a jerin ‘yan wasan da suka fi zira kwallo a gasar Ligue 1.

Duk da cewa ana yi masa kallon bai shahara sosai ba, hukumar FIFA ta sanya shi a jerin ‘yan wasa 23 da za a zabi zakaran dan kwallon duniya daga cikinsu.

Don haka ya kamata mu nada shi zakaran dan kwallon Afrika, ganin irin nasarorin da ya samu ba a kungiyarsa da ke Turai ba kawai, har ma da kasa da nahiyar Afrika baki daya.

Za ku iya zaban ne ta hanyar latsa wannan rariyar likau din da ke biye:

http://www.bbc.co.uk/worldservice/africa/2010/11/101111_afoy_2010_vote_page.shtml

Ko kuma ta lambar waya +44 7786200070