Iran ta baiwa Najeriya damar bincike

Iran ta baiwa Najeriyar damar bincike
Image caption Makaman da aka kama na ci gaba da jawo kace-nace

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana cewa gwamnatin Iran ta bata damar ganawa da dan Iran din da ake zargi na da hannu a shigowa da wadansu makamai Najeriya.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Mr. Odien Ajumogobia ya yi karin haske akan ganawar su da takwaransa na Iran game da kwantenonin da ke dauke da makamai da aka kama a tashar ruwan Lagos kwanakin baya.

A jawabin da Mr Odien Ajumogobia ya yiwa manema labarai, ya tabbatar da cewa kwantenonin da ke dauke da makaman sun samo asali ne daga Iran.

A baya ne dai hukumomin Najeriya suka bukaci ofishin jakadancin Iran a Najeriya da ya mika musu wani da ake zargi da hannu a al'amarin.

'Damar ganawa da dan Iran'

Lamarin da a wancan lokacin Ofishin jakadancin Iran din yace yawan kalamai a kan batun ka iya jawo rudani.

Mista Odien Ajumogobia ya bayyana cewa ganawarsu da takwaransa na Iran wato Manouchehr Mottak ta yi alfanu.

Ya kara da cewa an baiwa jami'an tsaron Najeriya damar ganawa da wani dan Iran wanda ake ganin cewa zai iya yin karin haske akan yanda aka shigo da makaman da kuma inda za'a kai su, da ma kuma ta yadda dan Najeriya ya shigo ciki.

Daya daga cikin wadanda ke da hannu a shigo da kayan dai dan kasar Iran ne, wanda Ministan ya bayyana cewa sun samu labarin ya yi gudun hijira zuwa ofishin jakadancin Iran da ke Dubai.

Ministan dai ya bayyana cewa har yanzu basu kammala bincike akan wannan sabon al'amarin ba.