Lampard ya kara samun rauni

Frank Lampard
Image caption Frank Lampard ya dade ba ya taka leda

Dan wasan Chelsea Frank Lampard zai shafe makwanni uku ba ya taka leda bayanda ya kara samun rauni a lokacin da yake horo.

Dan wasan mai shekaru 32, na fatan dawowa wasa ne a karawar da kungiyar za ta yi da Sunderland, bayan ya shafe fiye da watanni biyu yana jinya. Amma sai ya kara samun rauni lokacin da yake horo tare da sauran abokan wasansa ranar Alhamis, kuma yanzu ba zai warke ba sai watan Disamba.

Rabon Lampard da wasa tun karawar da Chelsea ta doke Stoke City da ci 2-0 a ranar 28 ga watan Agusta.