Ra'ayi Riga: Zubar da ciki ta haramtacciyar hanya

Wata mai ciki a kwance
Image caption Zubar da ciki inda ba a kware ba yana kai ga halaka

A wannan makon ne a Ghana, kwararru ta fuskar kiwon lafiya da sauran jami'ai daga kasashen Afirka, suka gudanar da taro a birnin Accra, domin duba yadda za a shawo kan matsalar mace-macen mata a lokacin da suke zubda ciki a nahiyar Afirka.

Wata kungiya mai zaman kanta, IPAS, tare da hadin gwiwar ma'aikatar lafiyar Ghana da kuma Majalisar Dinkin Duniya, su ne suka shirya taron.

Alkalumman da aka bayar a lokacin ganawar sun nuna cewa, mata kimanin dubu sittin da bakwai da rabi ne ke mutuwa a duk shekara a duniya, yayin zubda cikin.

Kuma fiye da rabinsu a nahiyar Afirka.

Sama da rabin matan da ke rasa ransu a Afirkar a lokacin zubda cikin, basu kai shekara ashirin da biyar a duniya ba.

An kuma bayyana cewa, mata miliyan biyar ne ake kwantarwa a asibiti a kowace shekara, a dukan fadin duniya, saboda matsalolin da ke biyo bayan zubar da ciki.

Fiye da miliyan guda daga cikinsu a nahiyar Afirka.

To shin yaya matsalar take a kasashenmu?

A filin Ra'ayi Riga na wannan makon, mun duba illar wadannan matsaloli, da abinda ke jawo su, da kuma hanyar da za a iya bi a magance su.