Kasashen G8 za su magance rikicin kudade

Taron kasashen G20 a Seoul
Image caption Yau ake shiga rana ta karshe a taron kasashen G8 dake gudana a Seoul, babban birnin kasar Korea ta Kudu

A karshen taronda suka gudanar a Seuol babban birnin Korea ta Kudu, shugabannin kasashen nan 20 masu karfin tattalin arziki sun amince su kaucewa gasar rage darajar kudadensu.

Shugabannin sun cimma yarjejeniyar fito da wasu ka'idoji da za su magance rashin daidaito a kasuwancin duniya, wanda suka ce yana kawo tarnaki ga ci gaban kasashe.

An dai samu tankiya tsakaniya wasu daga cikin mahalarta taron, a kan hanyoyin da ya kamata a bi wajen magance matsalolin da ake fama da su a manufofin kudi da na kasuwancin kasashen duniya.

Yayin taron dai an fuskanci takaddama dangane da batun nan na manufofin kasashen dangane da darajar kudadensu, inda wasu kasashe ke nuna damuwa game da yadda wasu kasashen ke rage darajar kudadensu da nufin karfafa fitar da kayan da suke kerawa zuwa kasawannin kasashen waje.

Sai dai sanarwar karshen taron ta yi kira ga wasu kasashen da ke kungiyar su daina dabi'ar nan ta rage darajar kudadensu da nufin jawo kasuwa ga kayan da suke kerawa.

Wasu dai na fargabar rikicin da ake samu tsakanin China da Amurka kan wadannan batutuwan na iya kawo tarnaki ga ci gaba.