Karancin ruwa na barazana ga harkokin kasuwanci

Ruwa
Image caption Karancin ruwa na barazana ga harkokin kasuwanci a duniya

Wani bincike da masana suka yi ya nuna cewa, kamfanoni na kara nuna damuwa dangane da karancin ruwa da bil'adama ke bukata.

Wani kamfanin masana dake bincike mai suna, Environmental Resources Management yace, rabin kusan dukkan kamfanoin da ya gana da su sun ce, mai yiwuwa a fuskanci matsalar ruwa nan da shekaru biyar masu zuwa

Tun ma kafin masanan su fidda wannan rahoto babban jam'in kimiyya na Birtaniya yayi kashedin cewa, matsalar karancin ruwa ita ce zata haddasa yawancin matsalolin muhalli da za'a fuskanta.

Ire iren kamfanonin da zasu fuskanci matsalar karancin ruwa kuwa sun hada da kamfanonin abinci dana abubuwan sha da kamfanonin karafa da kuma na hakar ma'adinai