An samu karuwar cutar amai da gudawa a Haiti

Cutar ami da gudawa a Haiti
Image caption An samu karuwar masu fama da cutar amai da gudawa a Kasar Haiti a cikin kwanaki uku

Kungiyar kiwon lafiya ta sa kai, wato Medicine San Frontiers tace, an samu karuwar wadanda suka kamu da cutar amai da gudawa, wato kwalara a cikin kwanakin ukun nan a kasar Haiti.

Kungiyar likitocin masu aikin sa kai ta kuma ce, yanzu haka dukkanin asibitocin dake babban birnin kasar ta Haiti, wato Port-au-Prince suna cike ne makil da wadanda ke fama da ciwon na kwalara.

A jiya jumma'a ne dai majalisar dinkin duniya ta nemi karin tallafin kudi domin shawo kan yaduwar cutar ta kwalara a kasar ta Haiti.