Sojin Najeriya za su kai hari Naija Delta

Dan bindigar yankin Naija Delta
Image caption Dan bindigar yankin Naija Delta

Rundunar sojin Najeriya ta yi gargadin cewa za ta kai farmaki a kan sansanonin ’yan bindigar dac ke yankin Neja Delta mai arzikin man fetur.

Babban kwamandan hafsoshin tsaro na kasar, Oluseyi Petinrin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta bukaci farar hular da ke zaune daura da sansanoni tsagerun na Naija Deltan da su tashi daga kauyukansu nan take.

Air Marshal Petinrin ya ce a shirye dakarunsa su ke su kai hari a kan tsagerun da ke kiran kansu masu fafutukar neman ’yanci.

Wannan farmaki dai shi ne zai zamo na farko da sojojin za su kai yankin na Naija Delta tun bayan da gwamnatin kasar ta yiwa tsagerun afuwa a watan Agustan bara.

Air Marshal Petinrin ya ce harin martai ne a kan kame wadansu ma’aikatan man fetur ’yan kasashen waje su bakwai da tsagerun suka yi a makon jiya da kuma harin da aka kai gidan mashawarcin Shugaba Goodluck Jonathan a kan Naija Delta ranar Alhamis din da ta gabata.

Ranar Juma’a dai dakarun tabbatar da tsaro a yankin na Naija Delta suka ce sun kai hari wani sansani da ke Jihar Bayelsa, inda suka yi musayar wuta da ’yan bindigar har suka kwace makaman ’yan bindigar da taswirorin rijiyoyi da kafe-kafen kamfanonin man fetur.