Za'a yiwa maza miliyan 2 shayi a Rwanda

Kasar Rwanda
Image caption Hukumomin lafiya a kasar Rwanda na shirin yiwa maza miliyan 2 shayi da nufin shawo kan cutar nan mai karya garkuwar jiki wato AIDS

Gwmnatin Rwanda tace, tana shirin yiwa maza miliyan biyu shayi cikin shekaru biyu dake tafe, da nufin shawo kan yaudwar cutar nan mai karya gwarkuwar jiki, wato AIDS.

Shugabar hukumar yaki da cutar ta AIDS a kasar, Dakta Anita Asiimwe, ta fadawa BBC cewa, wani bincike da aka yi ya nuna cewa, yiwa maza shayi yana taimakawa wajen rage yaduwar cutar ta AIDS a kasashen Afurka ta kudu da kuma Uganda

Kafin wannan lokaci dai a kasar ta Rwanda, babu al'adar nan ta yiwa maza shayi, kuma koda a yanzu ma sai anyi fadakarwa sosai kafin wasu su amince ayi musu.