Sako Aung San Suu Kyi ya faranta rai

Aung San Suu Kyi
Image caption Aung San Suu Kyi tana jawabi ga magoya bayanta

Mutane da dama ne da suka taru a kofar wani gida a birnin Rangoon suka cika da farin ciki.

A wannan gida ne dai aka yiwa mai fafutukar tabbatar da tsarin dimokuradiyya ta kasar Bama, Aung San Suu Kyi, daurin talala tun shekaru bakwai da suka wuce.

A yau ne kuma hukumomin sojin kasar ta Bama suka baiwa Aung San Suu Kyi 'yancin walwala.

Da wayewar gari ne magoya bayan Aung San Suu Kyi suka fara turuwa zuwa kofar gidan.

Da yawa daga cikinsu sun yi tunanin cewa ba da jimawa ba za a sako ta, to amma lokaci sai tafiya ya ke yi ba labari.

Mutanen dai ba su karaya ba suka ci gaba da zaman jira.

Can da rana sai wani mai kayan miya ya shiga gidan, da ya fito kuma, kasancewar an hana shi magana da kowa, sai ya yi nuni da yatsunsa guda uku.

Wannan ne ya sa mutanen suka zaci karfe uku za a sako ta; to amma har karfe ukun ta wuce ba labari.

Bayan minti talatin kuma sai yanayin wurin ya sauya saboda samun rahotannin cewa an cire shingayen da aka gitta a hanyar zuwa gidan da kuma cewa jami'ai sun shiga sun karanta mata takardar janye daurin talalar.

Da fitowarta magoya bayanta suka fara sowa suna ambaton sunanta, wasunsu ma har suna zubar da kwalla.

A karo na farko sun samu wani abin da ya faranta musu rai.

A jawabin da ta yi wa magoya bayan nata, ta ce wajibi ne su yi aiki tare domin cimma muradun su.

Ya zuwa yanzu babu alamar an gindaya wasu sharuda kafin a sako ta.