Amurka tayi wa kasar Isra'ila tayi

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Image caption Majalisar ministocin kasar Isra'ila zata saurari tayin da kasar Amurka tayi wa Isra'ilan nata dakatar da gina sabbin matsugunan yahudawa a yammacin kogin Jordan

A yau lahadi ne za'a gabatarwa majalisar ministocin Isra'ila wani tayi da Amurka ta yiwa kasar domin ta dakatar da gina sabbin matsugunnan yahudawa a yammacin kogin Jordan.

Amurkan dai ta bukaci Isra'ila ne ta dakatar da gina sabbin matsugunan yahudawan na tsawon kwanaki casa'in nan gaba.

Wannan dakatarwa ba zata shafi gabashin birnin Qudus ba.

Gwamnatin Amurka ta kwashe watanni biyu tana ta kokarin ganin ta farfado da tattaunawar zaman lafiyar da ta cije tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.