Kwamandan MEND ya nemi afuwar yan Naija Delta

MEND
Image caption 'Yan bindigar MEND

A Najeriya wani tsohon shugaban kungiyar masu fafutukar kwato 'yancin Naija Delta wato MEND, wanda ake kira Janar Boyloaf ya ce, ya na neman afuwa daga wurin jama'ar yankin dangane da yadda gwagwarmayar da suka yi a baya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Shi dai Boyloaf na daga cikin wadanda suka rungumi shirin afuwar da gwamnatin Najeriya ta yiwa 'yan bindigar yankin Niger Delta a bara.

A wata ziyara da ya kawo ofishin BBC da ke Abuja, Boyloaf wanda a yanzu yana daga cikin masu son ganin an samu zaman lafiya a yankin, ya ce shirin gwamnati na sasantawa da 'yan gwagwarmayar na samun nasara, duk kuwa da matsalolin da ake fuskanta.

Sai dai ya ce bai yi nadamar fafatawar da suka yi da dakarun gwamnati ba a wancan lokacin, kasancewar a cewarsa suna gwagwarmaya ne domin ceto yankin daga mummunan halin da yake ciki.