Aung San Suu Kyi zata yi jawabi ga magoya bayanta

Aung San Suu Kyi a lokacin da aka sake ta
Image caption Kowanne lokaci daga yanzu ne ake saran mai fafutukar wanzar da tsarin dimukradiyar kasar Burma, Aung San Suu Kyi zata yi jawabi ga gangamin magoya bayanta

Wani lokaci a yau ne ake sa ran jagorar fafutukar kafa dimukradiyya a kasar Burma, Aung San Suu Kyi zata yi jawabi ga gangamin magoya bayanta, bayan gwamnatin mulkin sojan kasar ta kawo karshen daurin talalar da aka yi mata a jiya Asabar.

Kafin ta yi jawabi ga magoya bayanta da kuma manema labarai, Aung San Suu Kyi tana kuma shirin ganawa da jami'an diflomasiyya, da kuma 'yan jam'iyyarta, a hedikwatar jam'iyyar dake birnin Rangoon.

A jiya ne dai aka sako Aung San Suu Kyi, wato mako guda kenan, bayan gwamnatin mulkin sojan Burma ta gudanar da wani zabe da ya sha suka sosai.

Kasashen duniya da dama ne suka yi marhabun da sako Aung San Suu Kyi.

Shugaba Obama na Amurka yace, yana daukarta a matsayin wata jaruma.

Shi kuma sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Ban Ki Moon, kira yayi ga gwamnatin mulkin sojan Burma, ta sako dukkan fursunonin siyasa a kasar.