ACN za ta kai majalisar kasa kotu

Tutar ACN
Image caption Jam'iyyar ACN ita ce jam'iyyar adawa ta biyu a Najeriya

A Najeriya jam'iyyar adawa ta Action Congress of Nigeria, ACN, za ta kai majalisun kasar kotu kan kudurin dokar da 'yan majalisun ke son zartarwa, da zai basu damar kasancewa mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyunsu.

Su dai 'yan adawar sun ce yunkurin majalisar na zartar da dokar barazana ce ga jam'iyyu, da kuma dimokaradiyyar kasar.

Sai dai 'yan majalisar sun ce idan suka zartar da dokar za a samu wanzuwar dimokaradiya da ingantaccen zabe a kasar.

Shi dai kudurin dokar ya haye karatu na biyu a zauren majalisun dokokin, inda daga nan ne za su yi zaman jin ra'ayin jama'a kafin su zartar da shi.

Sakataren jam'iyyar ACN na kasa, Dr Usman Bugaji, ya shaida wa wakilin BBC Nasidi Adamu Yahaya, cewa ba su da wani zabi illa su garzaya kotu domin kalubalantar matakin da 'yan majalisar ke son dauka.