Mahajjata na hawan Arfa a kasar Saudiyya

Image caption Masallacin Makkah

Ranar Litinin tara ga watan Zul Hijja, ita ce ranar da miliyoyin Musulmi da ke aikin Hajji a kasar Saudi Arabia ke hawan Arfa, wato daya daga cikin shika- shikan aikin Hajji.

A washegarin ranar ne kuma sauran Musulmai a duk fadin duniya su ke shagulgulan Sallar layya.

Malamai dai sun bayyana ranar tara ga watan Zul Hijja a matsayin ranar da tafi muhimmanci a cikin ranakun shekara, a addinin Musulunci.

Ustaz Hussaini Zakaria, wani malamin addinin Musulunci a Abuja, ya ce wannan rana na da matukar falala.

Da ga cikin irin ayyuka da suka kamata Musulmi su yi domin samun amfanin wannan rana, sun hada da yin azumi, ga wadanda basu samu damar zuwa aikin Hajji ba.